1 Peter 4

1Saboda haka, tunda yake Almasihu ya sha wuya a jiki, muma mu sha damara da wannan ra’ayi. Duk wanda ya sha wuya a jiki ya daina aikata zunubi. 2Wannan mutum kuma baya kara zaman biye wa muguwar sha’awar mutumtaka, amma sai dai nufin Allah dukkan sauran kwanakinsa a duniya.

3Gama lokaci ya wuce da zamu yi abin da al’ummai suke son yi, wato fajirci, mugayen sha‘awace-sha’awace, da buguwa da shashanci da shaye-shaye da bautar gumaku da abubuwan kyama. 4Suna tunanin bakon abu ku ke yi da ba kwa hada kai tare da su yanzu a yin wadannan abubuwa, sai suna zarginku. 5Za su bada lissafi ga wanda yake a shirye ya shari’anta masu rai da matattu. 6Shi yasa aka yi wa matattu wa’azin bishara, cewa ko da shike anyi masu shari’a cikin jikunan mutane, su rayu bisa ga Allah a ruhu.

7Karshen dukkan abubuwa yana gabatowa. Saboda haka, ku zama natsatsu, ku natsu cikin tunaninku domin yin addu’oi. 8Gaba da kome, ku himmatu wajen kaunar juna, domin kauna bata neman tona zunuban wadansu. 9Ku yi wa juna bakunta da abubuwa nagari ba tare da gunaguni ba.

10Yadda kowanne dayanku ya sami baiwa, kuyi amfani da su domin ku kyautata wa juna, kamar masu rikon amanar bayebaye na Allah, wanda ya ba mu hannu sake. 11Idan wani yana yin wa’azi, ya zamana fadar Allah ya ke fadi, idan wani yana hidima, ya yi da karfin da Allah ya ba shi, domin cikin dukkan abubuwa a daukaka Allah ta wurin Yesu Almasihu. Daukaka da iko nasa ne har abada abadin. Amin.

12Ya kaunatattu, kada ku zaci cewa matsananciyar wahalar da ta zo ta gwada ku bakon abu ne, ko kuma wani bakon abu ne yake faruwa a gareku. 13Amma muddin kuna tarayya da Almasihu cikin wahalarsa, ku yi murna, domin kuyi farin ciki da murna sa’adda za a bayyana daukakarsa. 14Idan ana zargin ku sabili da sunan Almasihu, ku masu albarka ne, domin Ruhun daukaka da Ruhun Allah ya tabbata a kanku.

15Amma kada kowannen ku ya sha wahala sabo da horon shi mai kisan kai ne, ko barawo, ko mamugunci, ko mai shisshigi. 16Amma in wani yana shan wahala sabili da shi na Almasihu ne, kada ya ji kunya, amma ya daukaka Allah a wannan sunan.

17Domin lokaci ya yi da shari’a za ta fara daga gidan iyalin Allah. Idan kuwa za a fara da mu, menene karshen wadanda suka ki biyayya da bisharar Allah? 18Idan mutum, “mai adalci ya tsira da kyar, to, me zai faru da marar bin Allah da mai zunubi kuma?” Sabo da haka bari wadanda suke shan wuya bisa ga nufin Allah, su mika rayukansu ga amintaccen Mahalicci suna kuma yin ayyuka nagari.

19

Copyright information for HauULB